11 Ƙasar ta sami zaman lafiya shekara arba'in sa'an nan Otniyel, ɗan Kenaz ya rasu.
12 Jama'ar Isra'ila kuma suka sāke yin zunubi a gaban Ubangiji, Ubangiji kuwa ya sa Eglon Sarkin Mowab ya yi ƙarfi, domin ya yi gaba da su.
13 Sai ya tattaro Amoriyawa da Amalekawa, ya je ya ci Isra'ilawa, ya mallaki birnin dabino, wato Yariko.
14 Isra'ilawa suka bauta wa Eglon Sarkin Mowab, shekara goma sha takwas.
15 Amma sa'ad da Isra'ilawa suka yi kuka ga Ubangiji, ya ba su wanda zai cece su, wato Ehud, ɗan Gera daga kabilar Biliyaminu, shi kuwa bahago ne. Isra'ilawa suka aika wa Eglon Sarkin Mowab da kyautai ta hannun Ehud.
16 Sai Ehud ya ƙera wa kansa takobi mai kaifi biyu, tsawonsa kamu guda. Ya yi ɗamara da shi wajen cinyarsa ta dama a ƙarƙashin tufafinsa.
17 Sa'an nan ya ɗauki kyautan, ya kai wa Eglon Sarkin Mowab. Eglon kuwa mai ƙiba ne.