2 Ya yi haka ne domin ya koya wa tsararrakin Isra'ila yaƙi, wato waɗanda ba su taɓa yin yaƙi a dā ba.
3 Al'umman da suka ragu a ƙasar su ne, birane biyar na Filistiyawa, da dukan Kan'aniyawa, da Sidoniyawa, da Hiwiyawa da suke zaune a Dutsen Lebanon, tun daga Dutsen Ba'alharmon har zuwa mashigin Hamat,
4 don a jarraba Isra'ilawa da su, a gani ko za su yi biyayya da umarnan Ubangiji da ya ba kakanninsu ta hannun Musa.
5 Saboda haka jama'ar Isra'ila suka zauna tare da Kan'aniyawa, da Hittiyawa, da Amoriyawa, da Ferizziyawa, da Hiwiyawa, da Yebusiyawa.
6 Suka yi aurayya da su, suka kuma yi sujada ga gumakansu.
7 Jama'ar Isra'ila kuwa suka manta da Ubangiji Allahnsu, suka yi masa zunubi, suka yi wa gumakan nan Ba'al da Ashtarot sujada.
8 Domin haka Ubangiji ya husata ƙwarai da Isra'ilawa, sai ya bashe su ga Kushan-rishatayim, Sarkin Mesofotamiya. Jama'ar Isra'ila kuwa suka bauta masa shekara takwas.