20 Ya ce mata, “Ki tsaya a ƙofar alfarwar, idan wani ya zo ya tambaye ki, ‘Ko akwai wani a nan?’ Sai ki ce, ‘Babu.’ ”
21 Amma Yayel, matar Eber, ta ɗauki turken alfarwa da guduma, ta yi sanɗa zuwa wurinsa, ta kafa masa turken a gindin kunne, ya zarce har ƙasa, a sa'ad da yake sharar barcin gajiya. Ya kuwa mutu.
22 Barak kuwa yana bin sawun Sisera. Da Yayel ta gan shi, sai ta fita, ta tarye shi, ta ce masa, “Ka zo, zan nuna maka inda mutumin da kake nema yake.” Ya shiga alfarwarta, sai ga Sisera nan kwance matacce da turke a gindin kunnensa.
23 A wannan rana Allah ya fatattaki Yabin Sarkin Kan'ana, a gaban Isra'ilawa.
24 Isra'ilawa suka yi ta tsananta wa Yabin Sarkin Kan'ana har suka hallaka shi.