8 Sa'ad da Isra'ilawa suka zaɓi baƙin alloli,Sai ga yaƙi a ƙasar.Ba a ga garkuwa ko mashiA wurin mutum dubu arba'in na Isra'ila ba.
9 Zuciyata tana wajen shugabannin yaƙi na Isra'ila,Da mutanen da suka ba da kansu da farin ciki.Yabo ya tabbata ga Ubangiji!
10 Ku ba da labari,Ku da kuke haye da fararen jakuna,Kuna zaune a shimfiɗu,Ku da dole ku tafi da ƙafa duk inda za ku.
11 Ku kasa kunne! Da hayaniya mutane a bakin rijiyoyiSuna ba da labarin nasarar Ubangiji,Wato nasarar jama'ar Isra'ila!Sa'an nan jama'ar UbangijiSuna tahowa daga biranensu.
12 Ki ja gaba, ke Debora, ki ja gaba!Ki ja gaba! Ki raira waƙa, ki ja gaba!Ka ci gaba, kai Barak,Ɗan Abinowam, ka tasa kamammunka gaba!
13 Sa'an nan amintattu sun zo wurin shugabanninsu,Jama'ar Ubangiji suka zo wurina a shirye domin yaƙi.
14 Daga Ifrraimu mutane suka gangaro zuwa kwari,Bayan kabilar Biliyaminu da mutanenta.Daga Makir shugabannin sojoji suka zo,Daga Zabaluna kuma jarumawa suka gangaro.