14 zai shayar da ƙasarku da ruwa a kan kari, da ruwan bazara da na kaka. Za ku tattara sabon hatsinku da sabon ruwan inabinku, da manku.
15 Zai sa ciyawa ta tsiro a saurukanku domin dabbobinku. Za ku ci ku ƙoshi.
16 Ku lura fa, kada zuciya ta ruɗe ku, har ku kauce, ku bauta wa waɗansu alloli, ku yi musu sujada,
17 don kada Ubangiji ya yi fushi da ku, ya rufe sammai, ku rasa ruwa, ƙasa kuma ta kāsa ba da amfaninta, da haka za ku murmutu nan da nan a kyakkyawar ƙasar da Ubangiji yake ba ku.
18 “Sai ku riƙe zantuttukan nan nawa a zuciyarku da ranku. Za ku ɗaura su alama a hannuwanku, da goshinku.
19 Za ku koya wa 'ya'yanku su, ku yi ta haddace su, sa'ad da kuke zaune a gida, da sa'ad da kuke tafiya, da sa'ad da kuke kwance, da sa'ad da kuka tashi.
20 Za ku rubuta su a madogaran ƙofofin gidajenku, da bisa ƙofofinku,