21 don kwanakinku da kwanakin 'ya'yanku su yi tsawo a ƙasar da Ubangiji ya rantse wa kakanninku zai ba su muddin samaniya tana bisa duniya.
22 “Idan dai za ku lura, ku kiyaye dukan umarnan nan waɗanda nake umartarku ku kiyaye, ku ƙaunaci Ubangiji Allahnku, ku yi tafiya a dukan hanyoyinsa, ku manne masa,
23 sa'an nan Ubangiji zai kori al'umman nan duka a gabanku. Za ku kori al'umman da suka fi ku yawa da ƙarfi.
24 Duk inda tafin ƙafarku ya taka kuma zai zama naku. Iyakarku za ta kama daga jeji zuwa Lebanon da kuma daga Kogin Yufiretis zuwa Bahar Rum.
25 Ba mutumin da zai iya tsayayya da ku. Ubangiji Allahnku zai sa ƙasar ta firgita, ta ji tsoronku a duk inda kuka sa ƙafa, kamar yadda ya faɗa muku.
26 “Ga shi, yau, na sa albarka da la'ana a gabanku.
27 Za ku sami albarka idan kun yi biyayya da umarnan Ubangiji Allahnku waɗanda nake umartarku da su yau.