1 “Idan aka iske gawar mutum wanda wani ya kashe a fili a ƙasar da Ubangiji Allahnku ya ba ku, ku mallaka, ba a kuwa san wanda ya kashe shi ba,
2 sai dattawanku da alƙalanku su fito su auna nisan wurin daga gawar zuwa garuruwan da yake kewaye da gawar.
3 Dattawan garin da ya fi kusa da gawar za su ɗauki karsana wadda ba a taɓa aiki da ita ba, ba a kuma taɓa sa mata karkiya ba.
4 Sai dattawan garin nan su kai karsanar kwari inda ruwa yake gudu, inda ba a taɓa noma ko shuka ba. A can cikin kwarin za a karya wuyan karsanar.