6 Sai dukan dattawan garin da ya fi kusa da gawar su wanke hannuwansu a bisa karsanar da aka karya wuyanta a kwarin.
7 Sa'an nan su ce, ‘Hannuwanmu ba su zub da wannan jini ba, idanunmu kuma ba su ga wanda ya zubar da shi ba.
8 Ya Ubangiji, ka kuɓutar da jama'arka, Isra'ila, wadda ka fansa, kada ka bar alhakin jinin marar laifin nan ya kama jama'arka, Isra'ila. Ka gafarta musu alhakin wannan jini.’
9 Ta haka za ku kawar da alhakin jinin marar laifi daga cikinku, sa'ad da kuka yi abin da yake daidai a wurin Ubangiji.”
10 “Sa'ad da kuka tafi yaƙi da magabtanku, Ubangiji Allahnku kuwa ya bashe su a hannunku, kun kuwa kama su bayi,
11 in a cikinsu ka ga wata kyakkyawar mace wadda ka yi sha'awarta, to, ka iya aurenta.
12 Sai ka kawo ta gidanka, ta aske kanta, ta yanke farcenta,