11 “Kada ku sa rigar da aka saƙa da ulu garwaye da lilin.
12 “Sai ku yi wa rigar da kukan sa tuntu huɗu, tuntu ɗaya a kowace kusurwa.
13 “Idan mutum ya auri mace, ya shiga wurinta, sa'an nan ya ƙi ta,
14 yana zarginta da cewa ta yi abin kunya, yana ɓata mata suna a fili, yana cewa, ‘Na auri wannan mata, amma sa'ad da na kusace ta, sai na iske ita ba budurwa ba ce,’
15 sai mahaifinta da mahaifiyarta su kawo shaidar budurcin yarinyar a gaban dattawan garin a dandalin ƙofar garin.
16 Sai mahaifinta ya ce wa dattawan, ‘Na ba wannan mutum 'yata aure, amma ya ƙi ta.
17 Yana zarginta da aikata abin kunya, ya ce, bai iske 'yarmu budurwa ba. Amma ga shaidar budurcin 'yata.’ Sai su shimfiɗa tsalala a gaban dattawan.