16 Sai mahaifinta ya ce wa dattawan, ‘Na ba wannan mutum 'yata aure, amma ya ƙi ta.
17 Yana zarginta da aikata abin kunya, ya ce, bai iske 'yarmu budurwa ba. Amma ga shaidar budurcin 'yata.’ Sai su shimfiɗa tsalala a gaban dattawan.
18 Sai dattawan garin su kama mutumin su yi masa bulala,
19 su ci shi tara shekel ɗari na azurfa, su ba mahaifin yarinyar, gama a fili mutumin ya ɓata sunan budurwar cikin Isra'ila. Za ta zama matarsa, ba shi da iko ya sake ta muddin ransa.
20 “Idan aka tabbatar zargin gaskiya ne, ba a kuma ga shaidar budurcinta ba,
21 sai a kai yarinyar a ƙofar gidan mahaifinta, sa'an nan mutanen garin su jajjefe ta da duwatsu har ta mutu, don ta yi aikin wauta cikin Isra'ila, gama ta yi karuwanci a gidan mahaifinta. Ta haka za ku kawar da mugunta daga cikinku.
22 “Idan aka iske wani yana kwance da matar wani, sai a kashe dukansu biyu, wato mutumin da matar. Haka za ku kawar da mugunta daga Isra'ila.