2 Idan mutumin ba kusa da ku yake zaune ba, ko kuma ba ku san shi ba, to, sai ku kawo dabbar a gidanku, ta zauna a wurinku, har lokacin da mutumin ya zo ya shaida ta, sa'an nan ku ba shi.
3 Haka nan kuma za ku yi da jakinsa, da riga, da kowane abin wani da ya ɓace, ku kuwa kuka tsinta. Faufau, kada ku ƙyale su.
4 “Idan kun ga jakin wani ko sansa ya faɗi a hanya, kada ku ƙyale shi, sai ku taimake shi ku tashe shi.
5 “Kada mace ta sa suturar maza, kada kuma namiji ya sa suturar mata. Duk mai yin haka, abin ƙyama ne ga Ubangiji Allahnku.
6 “Idan kuna tafiya a hanya, kun ga sheƙar tsuntsu a itace, ko a ƙasa, da 'ya'yanta, ko da ƙwayaye a ciki, uwar kuma tana kwance bisa 'ya'yan ko ƙwayayen, kada ku kama uwar duk da 'ya'yan.
7 Sai ku bar uwar ta tafi, amma kun iya kwashe 'ya'yan. Yin haka zai sa ku sami zaman lafiya da tsawon rai.
8 “Sa'ad da kuka gina sabon gida, sai ku ja masa rawani don kada ku jawo wa gidanku alhakin jini idan wani ya fāɗi daga bisa.