9 “Kada ku shuka iri biyu a gonar inabinku don kada abin da kuka shuka da amfanin gonar inabinku su zama haramiyarku.
10 “Kada ku haɗa sa da jaki su yi huɗa tare.
11 “Kada ku sa rigar da aka saƙa da ulu garwaye da lilin.
12 “Sai ku yi wa rigar da kukan sa tuntu huɗu, tuntu ɗaya a kowace kusurwa.
13 “Idan mutum ya auri mace, ya shiga wurinta, sa'an nan ya ƙi ta,
14 yana zarginta da cewa ta yi abin kunya, yana ɓata mata suna a fili, yana cewa, ‘Na auri wannan mata, amma sa'ad da na kusace ta, sai na iske ita ba budurwa ba ce,’
15 sai mahaifinta da mahaifiyarta su kawo shaidar budurcin yarinyar a gaban dattawan garin a dandalin ƙofar garin.