1 “Duk wanda aka dandaƙe ko wanda aka yanke gabansa ba zai shiga taron jama'ar Ubangiji ba.
2 “Shege ba zai shiga taron jama'ar Ubangiji ba. Har tsara ta goma zuriyarsa ba za su shiga taron jama'ar Ubangiji ba.
3 “Kada Ba'ammone ko Bamowabe ya shiga taron jama'ar Ubangiji. Har tsara ta goma ta zuriyarsu ba za su shiga taron jama'ar Ubangiji ba.
4 domin ba su zo sun tarye ku, su kawo muku abinci da ruwa ba sa'ad da kuke a hanyarku, lokacin da kuka fito daga Masar. Ga shi kuma, sun yi ijara da Bal'amu ɗan Beyor daga Fetor ta Mesofatamiya ya zo ya la'anta ku.