5 Amma Ubangiji Allahnku ya ƙi saurarar Bal'amu, sai Ubangiji ya juyar da la'anar ta zama muku albarka saboda Ubangiji Allahnku yana ƙaunarku.
6 Har abada kada ku nemar musu zaman lafiya ko wadata.
7 “Kada ku ji ƙyamar Ba'edome gama shi danginku ne. Kada kuma ku ji ƙyamar Bamasare don kun yi baƙunci a ƙasarsa.
8 'Ya'yansu tsara ta uku, za su iya shiga taron jama'ar Ubangiji.”
9 “Sa'ad da kuka kafa sansani don ku yi yaƙi da magabtanku, sai ku kiyaye kanku daga kowane mugun abu.
10 Idan wani a cikinku ya ƙazantu saboda ya zubar da maniyyi da dare, to, sai ya fita daga sansanin, kada ya koma sansanin.
11 Amma da maraice, sai ya yi wanka da ruwa, ya koma sansani sa'ad da rana ta faɗi.