1 “Idan wata gardama ta tashi tsakanin mutane, suka je gaban shari'a, alƙalai kuwa suka yanke musu maganar, suka kuɓutar da marar laifi, suka kā da mai laifin,
2 idan mai laifin ya cancanci bulala, sai alƙali ya sa shi ya kwanta ƙasa, a bulale shi a gabansa daidai yawan bulalar da ta dace da irin laifin da ya yi.
3 Za a iya yi masa bulala arba'in, amma kada ta fi haka, don kada a ci gaba da bugunsa fiye da haka, har ya zama rainanne a idonku.
4 “Kada ku yi wa takarkari takunkumi sa'ad da yake tattaka hatsinku.”
5 “Idan 'yan'uwa suna zaune wuri ɗaya tare, in ɗayansu ya rasu bai haihu ba, to, kada matar marigayin ta auri wani baƙo wanda yake ba a cikin dangin mijin ba. Sai ɗan'uwan mijinta ya zo wurinta, ya aure ta, ya yi mata abin da ya kamaci ɗan'uwan miji ya yi.
6 Ɗan farin da za ta haifa, zai zama magajin marigayin don kada a manta da sunansa cikin Isra'ila.
7 Amma idan mutum ya ƙi ya auri matar ɗan'uwansa, marigayi, sai matar ta tafi wurin dattawa a dandalin ƙofar gari, ta ce, ‘Ɗan'uwan mijina, marigayi, ya ƙi wanzar da sunan ɗan'uwansa cikin Isra'ila, gama ya ƙi yi mini abin da ya kamaci ɗan'uwan marigayi, ya yi.’