9 Ubangiji ya kawo mu nan, ya ba mu ƙasar nan, ƙasar da take mai yalwar abinci.
10 Ga shi, yanzu mun kawo nunan fari na amfanin ƙasar, da kai, ya Ubangiji, ka ba mu.’“Sai ku ajiye shi a gaban Ubangiji Allahnku, ku yi sujada a gaban Ubangiji Allahnku.
11 Ku yi murna kuma, ku da Lawiyawa, da baƙin da suke zaune tare da ku, saboda dukan alherin da Ubangiji Allah ya yi muku, ku da gidanku.
12 “Sa'ad da kuka gama fitar da zakarku ta amfanin gona a shekara ta uku, wadda take shekara ta fid da zaka, sai ku ba Balawe, da baƙo, da maraya, da matar da mijinta ya rasu, don su ci, su ƙoshi a cikin garuruwanku.
13 Sa'an nan za ku ce a gaban Ubangiji Allahnku, ‘Na fitar da tsattsarkan kashi daga cikin gidana na ba Balawe, da baƙo, da maraya, da matar da mijinta ya rasu bisa ga umarnin da ka yi mini. Ban karya wani umarninka ba, ban kuwa manta da su ba.
14 Ban ci kome daga cikin zakar sa'ad da nake baƙin ciki ba, ban kuma fitar da kome daga cikinta ba sa'ad da nake da ƙazanta, ban kuma miƙa wa matattu kome daga cikinta ba. Na yi biyayya da muryar Ubangiji Allahna, na aikata dukan abin da ka umarce ni.
15 Ka duba ƙasa daga Sama, daga wurin zamanka mai tsarki, ka sa wa jama'arka, Isra'ila, albarka duk da ƙasar da ka ba mu, ƙasar da take mai yalwar abinci, kamar yadda ka rantse wa kakanninmu.’ ”