14 Sa'an nan Lawiyawa za su ta da murya, su ce wa dukan Isra'ilawa:
15 “ ‘La'ananne ne mutumin da ya sassaƙa, ko ya ƙera gumaka, abar ƙyama ce ga Ubangiji, aikin hannun mai sana'a, ya kafa ta a ɓoye.’“Sai dukan jama'a su amsa, ‘Amin, Amin!’
16 “ ‘La'ananne ne wanda ya raina mahaifinsa ko mahaifiyarsa.’“Sai dukan jama'a su amsa, ‘Amin, Amin!’
17 “ ‘La'ananne ne wanda ya ci iyakar maƙwabcinsa.’“Sai dukan jama'a su amsa, ‘Amin, Amin!’
18 “ ‘La'ananne ne wanda ya karkatar da makaho daga hanya.’“Sai dukan jama'a su amsa, ‘Amin, Amin!’
19 “ ‘La'ananne ne wanda ya yi wa baƙo, ko maraya, ko gwauruwa ta gaske shari'a ta rashin gaskiya.’“Sai dukan jama'a su amsa, ‘Amin, Amin!’
20 “ ‘La'ananne ne wanda ya kwana da matar mahaifinsa, gama ya buɗe fatarin matar mahaifinsa.’“Sai dukan jama'a su amsa, ‘Amin, Amin!’