14 idan kuma ba ku kauce zuwa dama ko hagu daga maganar da na umarce ku da ita yau ba, wato don ku bi waɗansu gumaka, ku bauta musu.”
15 “Amma idan ba za ku yi biyayya da Ubangiji Allahnku ba, ko kuwa ba ku lura kuka aikata umarnansa da dokokinsa waɗanda nake umartar da su yau ba, to, dukan waɗannan la'ana za su auko muku, su same ku.
16 “La'anannu za ku zama a gari da karkara.
17 “La'anannu ne kwandunanku da makwaɓan ƙullunku.
18 “La'anannu ne 'ya'yanku, da amfanin gonakinku, da 'ya'yan shanunku, da 'ya'yan tumakinku da na awakinku.
19 “Da la'ana za ku shiga, da la'ana kuma za ku fita.
20 “Ubangiji zai aiko muku da la'ana, da ruɗewa, da damuwa cikin dukan abin da za ku yi, har ya hallaka ku, ku lalace da sauri saboda mugayen ayyukanku, domin kuma kuka rabu da ni.