26 “Amma Ubangiji ya yi fushi da ni saboda ku, don haka bai ji ni ba. Ya ce mini, ‘Ya isa. Kada ma ka sāke yi mini magana a kan wannan al'amari.
27 Ka hau kan ƙwanƙolin Dutsen Fisga, ka dubi gabas, da yamma, da kudu, da arewa. Ka dubi ƙasar da idanunka, gama ba za ka haye Urdun ba.
28 Amma ka umarci Joshuwa, ka ƙarfafa shi. Shi ne zai jagorar jama'ar nan, su haye, shi ne kuma wanda zai rarraba musu gādon ƙasar da za ka gani.’
29 “Sai muka zauna a kwari daura da Bet-feyor.”