1 “Sa'ad da duk waɗannan abubuwa suka same ku, wato albarka da la'ana waɗanda na sa a gabanku, in kun tuna da su a zuciyarku a duk inda kuke cikin al'ummai inda Ubangiji Allahnku ya kora ku,
2 kuka sāke komowa wurin Ubangiji Allahnku, ku da 'ya'yanku kuka yi biyayya da maganarsa da zuciya ɗaya, da dukan ranku, bisa ga yadda na umarce ku yau,
3 sa'an nan Ubangiji Allahnku zai komo da ku daga bauta, ya yi muku jinƙai. Zai tattaro ku daga cikin al'ummai inda ya warwatsa ku.
4 Idan korarrunku suna can ƙurewar duniya, Ubangiji Allahnku zai tattaro ku daga can, ya dawo da ku.
5 Ubangiji Allahnku kuma zai komo da ku cikin ƙasar da kakanninku suka mallaka, za ku mallake ta. Ubangiji zai arzuta ku, ya riɓaɓɓanya ku fiye da kakanninku.