2 kuka sāke komowa wurin Ubangiji Allahnku, ku da 'ya'yanku kuka yi biyayya da maganarsa da zuciya ɗaya, da dukan ranku, bisa ga yadda na umarce ku yau,
3 sa'an nan Ubangiji Allahnku zai komo da ku daga bauta, ya yi muku jinƙai. Zai tattaro ku daga cikin al'ummai inda ya warwatsa ku.
4 Idan korarrunku suna can ƙurewar duniya, Ubangiji Allahnku zai tattaro ku daga can, ya dawo da ku.
5 Ubangiji Allahnku kuma zai komo da ku cikin ƙasar da kakanninku suka mallaka, za ku mallake ta. Ubangiji zai arzuta ku, ya riɓaɓɓanya ku fiye da kakanninku.
6 Ubangiji Allahnku kuma zai tausasa zuciyarku da ta 'ya'yanku domin ku ƙaunaci Ubangiji Allahnku da zuciya ɗaya da dukan ranku, domin ku rayu.
7 Ubangiji Allahnku kuwa zai ɗora wa magabtanku da maƙiyanku waɗanda suka tsananta muku waɗannan la'ana.
8 Sa'an nan za ku yi biyayya da maganar Ubangiji Allahnku, ku kiyaye dukan umarnan nan waɗanda na umarce ku da su yau.