1 “Ku saurara, ya ku sammai, gama zan yi magana,Bari duniya ta ji maganar bakina.
2 Bari koyarwata ta zubo kamar ruwan sama,Maganata ta faɗo kamar raɓa,Kamar yayyafi a bisa ɗanyar ciyawa,Kamar ɗiɗɗigar ruwa a bisa ganyaye.
3 Gama zan yi shelar sunan Ubangiji,In yabi girman Allahnmu!
4 “Shi Dutse ne, aikinsa kuma cikakke ne,Gama dukan hanyoyinsa masu adalci ne.Allah mai aminci ne, babu rashin gaskiya a gare shi,Shi mai adalci ne, nagari ne kuma.
5 Sun aikata mugunta a gabansa,Su ba 'ya'yansa ba ne saboda lalacewarsu,Su muguwar tsara ce, karkatacciya,