24 Za su lalace saboda yunwa,Zazzaɓi mai zafi, da muguwar annoba za su cinye su.Zan aika da haƙoran namomi a kansu,Da dafin abubuwa masu jan ciki.
25 Waɗanda suke a waje, takobi zai kashe su,A cikin ɗakuna kuma tsoro,Zai hallaka saurayi da budurwa,Da mai shan mama da mai furfura.
26 Na ce, “Zan watsar da su,In sa a manta da su cikin mutane.”
27 Amma saboda gudun tsokanar maƙiyi,Kada abokan gābansu su zaci su ne suka ci nasara.Ai, ni ne na yi wannan.’
28 “Gama su al'umma ce wadda ba ta yin shawara,Ba su da ganewa.
29 Da suna da hikima, da sun gane wannan,Da za su gane da yadda ƙarshensu zai zama!
30 Ƙaƙa mutum ɗaya zai runtumi dubu,Mutum biyu kuma su kori zambar goma,Sai dai Dutsensu ya sayar da su,Ubangiji kuma ya bashe su?