32 Kurangar inabinsu daga kurangar inabin Saduma neDa gonakin Gwamrata.'Ya'yan inabinsu dafi ne,Nonnansu masu ɗaci ne.
33 Ruwan inabinsu dafin macizai ne.Da mugun dafin kumurci.
34 “ ‘Wannan ba a jibge suke a rumbunana ba,A ƙulle kuma a taskokina?
35 Sakayya da ɗaukar fansa nawa ne,A lokacin ƙafarsu za ta zame,Gama ranar masifarsu ta kusa,Hallakarsu za ta zo da sauri.’
36 Ubangiji zai ɗauka wa jama'arsa fansa,Zai ji ƙan bayinsa,Sa'ad da ya ga ƙarfinsu ya kāsa,Ba kuma wanda ya ragu, bawa ko ɗa.
37 Sa'an nan zai ce, ‘Ina gumakansu,Dutse wanda suka nemi mafaka gare shi,
38 Waɗanda suka ci kitsen hadayunsu,Suka sha ruwan inabin hadayarsu ta sha?Bari su tashi su taimake ku,Bari su zama mafaka!