42 Zan sa kibauna su bugu da jini,Takobina zai ci nama,Da jinin kisassu da na kamammu,Da ƙoƙon kan shugabannin maƙiya.’
43 “Ya ku al'ummai, ku yabi jama'arsa,Gama zai rama wa bayinsa saboda jininsu,Zai ɗauki fansa a kan magabtansa,Zai tsarkake ƙasar jama'arsa.”
44 Sai Musa da Joshuwa ɗan Nun suka zo, suka hurta dukan kalmomin wannan waƙa a kunnen jama'a.
45 Sa'ad da Musa ya gama hurta waɗannan kalmomi ga Isra'ila,
46 ya ce musu, “Ku riƙe dukan waɗannan kalmomi a zuciyarku, waɗanda nake yi muku kashedi da su a yau don ku umarci 'ya'yanku su kiyaye dukan maganar dokokin nan sosai.
47 Wannan ba magana kurum ba ce, amma ranku ne. Ta wurin wannan magana ce za ku yi tsawon rai a ƙasar da za ku haye Urdun zuwa ciki don ku mallake ta.”
48 A wannan rana ce Ubangiji ya ce wa Musa,