1 Wannan ita ce albarkar da Musa, mutumin Allah, ya sa wa Isra'ilawa kafin ya rasu.
2 Ya ce,“Ubangiji ya taho daga Sina'i,Daga Dutsen Faran kuma ya haskaka,Ya taho tare da dubban tsarkakansa,Da harshen wuta a damansa.
3 Hakika, yana ƙaunar jama'arsa,Dukan tsarkaka suna a ikonka,Suna biye da kai,Suna karɓar umarninka.
4 Musa ya ba mu dokoki,Abin gādo ga taron jama'ar Yakubu.
5 Ubangiji shi ne sarki a Yeshurun,Sa'ad da shugabanni suka taru,Dukan kabilan Isra'ila suka taru.
6 “Allah ya sa Ra'ubainu ya rayu, kada ya mutu,Kada mutanensa su zama kaɗan.”
7 A kan Yahuza ya ce,“Ka ji muryar Yahuza, ya Ubangiji,Ka kawo shi wurin jama'arsa.Ka yi yaƙi da ikonka dominsu,Ka taimake shi a kan maƙiyansa.”