35 An nuna muku wannan don ku sani Ubangiji shi ne Allah, banda shi, ba wani kuma.
36 Ya sa ku ji muryarsa daga Sama don ya horar da ku. Ya kuma sa ku ga babbar wutarsa a duniya, kuka kuma ji muryarsa daga cikin wutar.
37 Saboda ya ƙaunaci kakanninku shi ya sa ya zaɓi zuriyarsu a bayansu, shi kansa kuma ya fisshe ku daga Masar da ikonsa mai girma.
38 Ya kori al'ummai a gabanku waɗanda suka fi ku girma da iko, ya kawo ku a ƙasarsu, ya ba ku ita abar gādo kamar yadda yake a yau.
39 Domin haka, yau sai ku sani, ku kuma riƙe a zuciyarku, cewa Ubangiji shi kaɗai ne Allah a sama da duniya. Banda shi, ba wani kuma.
40 Sai ku kiyaye dokokinsa da umarnansa waɗanda na umarce ku da su yau, don zaman lafiyarku da na 'ya'yanku a bayanku, domin kuma ku yi tsawon rai a ƙasa wadda Ubangiji Allahnku yake ba ku har abada.”
41 Sai Musa ya keɓe birane uku a hayin gabashin Urdun,