45 su ne kalmomi, da dokoki, da farillai, waɗanda Musa ya faɗa wa jama'ar Isra'ila, bayan da sun fito Masar,
46 a hayin Urdun a kwari daura da Bet-feyor, a ƙasar Sihon, Sarkin Amoriyawa, mazaunan Heshbon, waɗanda Musa da Isra'ilawa suka ci da yaƙi sa'ad da suka fita daga ƙasar Masar.
47 Suka mallaki ƙasar Sihon, da ƙasar Og, Sarkin Bashan, sarakuna biyu na Amoriyawa waɗanda suke a hayin gabashin Urdun.
48 Ƙasar ta kama daga Arower wanda yake a kwarin kogin Arnon zuwa dutsen Siriyon, wato Harmon,
49 da dukan Araba a hayin gabashin Urdun, har zuwa tekun Araba a gindin gangaren Fisga.