2 don ku ji tsoron Ubangiji Allahnku, ku da 'ya'yanku da jikokinku, ku kuma kiyaye dukan dokokinsa da umarnansa, waɗanda nake umartarku dukan kwanakinku don ku yi tsawon rai.
3 Don haka, ku ji, ya Isra'ilawa, ku lura, ku kiyaye su domin zaman lafiyarku, domin kuma ku riɓaɓɓanya ƙwarai a ƙasar da take mai yalwar abinci yadda Ubangiji Allah na kakanninku ya alkawarta muku.
4 “Ku ji, ya Isra'ilawa, Ubangiji shi ne Allahnmu, Ubangiji ɗaya ne.
5 Sai ku ƙaunaci Ubangiji Allahnku da zuciya ɗaya, da dukan ranku, da dukan ƙarfinku.
6 Waɗannan kalmomi da na umarce ku da su a yau, za su zauna a zuciyarku.
7 Sai ku koya wa 'ya'yanku su da himma. Za ku haddace su sa'ad da kuke zaune a gida, da sa'ad da kuke tafiya, da sa'ad da kuke kwance, da sa'ad da kuka tashi.
8 Za ku ɗaura su a hannunku da goshinku don alama.