2 Dukan wuraren zaman Yakubu,Ubangiji ya hallakar ba tausayi,Da fushinsa kuma ya rurrushe kagaran Sihiyona.Ya ƙasƙantar da mulki da masu mulkin.
3 Da zafin fushinsa, ya karya ƙarfin Isra'ila,Ya kuma bar yi musu taimakoA lokacin da abokan gāba suka zo.Kamar harshen wuta, ya ƙone dukan abin da yake na Yakubu.
4 Ya ja bakansa kamar abokan gāba,Ya kuma nuna ikonsa kamar maƙiyi.Ya hallaka dukan abin da yake da bansha'awa.A alfarwar Sihiyona, ya zubo da hasalarsa kamar wuta.
5 Ubangiji ya zama kamar maƙiyi, ya hallaka Isra'ila.Ya hallaka fādodinta duka,Ya mai da kagaranta kango.Ya aukar wa Yahuza da makoki da baƙin ciki mai yawa.
6 Ya rushe Haikalinsa kamar bukka cikin gona,Ya mai da wurin yin ƙayyadaddun idodinsa kufai.Ubangiji ya sa ƙayyadadden idi da kiyaye AsabarSu ƙare a Sihiyona,Da zafin fushinsa kuma ya wofinta sarki da firist.
7 Ubangiji ya wulakanta bagadensa,Ya kuma wofinta tsattsarkan Haikalinsa.Ya ba da garun fādodinta a hannun abokan gāba,Suka yi sowa a Haikalin UbangijiKamar a ranar idi.
8 Ubangiji ya yi niyyaYa mai da garun Sihiyona kufai,Ya auna ta da igiyar awo,Bai janye dantsensa daga hallaka ta ba.Ya sa kagara da garu su zozaye, su lalace tare.