4 Ya ja bakansa kamar abokan gāba,Ya kuma nuna ikonsa kamar maƙiyi.Ya hallaka dukan abin da yake da bansha'awa.A alfarwar Sihiyona, ya zubo da hasalarsa kamar wuta.
5 Ubangiji ya zama kamar maƙiyi, ya hallaka Isra'ila.Ya hallaka fādodinta duka,Ya mai da kagaranta kango.Ya aukar wa Yahuza da makoki da baƙin ciki mai yawa.
6 Ya rushe Haikalinsa kamar bukka cikin gona,Ya mai da wurin yin ƙayyadaddun idodinsa kufai.Ubangiji ya sa ƙayyadadden idi da kiyaye AsabarSu ƙare a Sihiyona,Da zafin fushinsa kuma ya wofinta sarki da firist.
7 Ubangiji ya wulakanta bagadensa,Ya kuma wofinta tsattsarkan Haikalinsa.Ya ba da garun fādodinta a hannun abokan gāba,Suka yi sowa a Haikalin UbangijiKamar a ranar idi.
8 Ubangiji ya yi niyyaYa mai da garun Sihiyona kufai,Ya auna ta da igiyar awo,Bai janye dantsensa daga hallaka ta ba.Ya sa kagara da garu su zozaye, su lalace tare.
9 Ƙofofinta sun nutse ƙasa,Ya lalatar, ya kakkarya ƙyamarenta,An kai sarkinta da mahukuntanta cikin al'ummai,Inda ba a bin dokokin annabawanta,Ba su kuma samun wahayi daga wurin Ubangiji.
10 Dattawan Sihiyona suna zaune a ƙasa shiru,Sun yi hurwa, suna saye da tufafin makoki.'Yan matan Urushalima kuma sun sunkuyar da kansu ƙasa.