1 Ubangiji ya yi magana da Mika mutumin Moreshet a zamanin Yotam, da na Ahaz, da na Hezekiya, sarakunan Yahuza. Ya yi masa magana a kan Samariya da Urushalima.
2 Dukanku ku ji, ku al'ummai!Ki kasa kunne, ya duniya, da dukanabin da yake cikinki.Bari Ubangiji AllahDaga Haikalinsa mai tsarki ya zamashaida a kanku.
3 Ga shi, Ubangiji yana fitowa dagawurin zamansa,Zai sauko, ya taka kan tsawawanduwatsun duniya.
4 Duwatsu za su narke aƙarƙashinsa,Kwaruruka za su tsattsage kamarkakin zuma a gaban wuta,Kamar ruwa yana gangarowa dagatsauni.