1 Ni kuwa na ce, “Ku ji, ya kushugabannin mutanen Yakubu,Da ku sarakunan Isra'ila.Ya kamata ku san shari'a.
2 Amma kuna ƙin nagarta, kunaƙaunar mugunta,Kuna feɗe mutanena,Kuna kuma fizge naman jikinsu dagaƙasusuwansu.
3 Kuna cin naman mutanena, kunafeɗe fatar jikinsu,Kuna kakkarya ƙasusuwansu,Kuna yanyanka su gunduwagunduwa kamar naman da za a saa tukunya.”
4 Sa'an nan za su yi kuka ga Ubangiji,Amma Ubangiji ba zai amsa musuba.Zai ɓoye musu fuskarsa a wannanlokaci,Saboda mugayen ayyukansu.
5 Ga abin da Ubangiji ya ce a kanannabawan da suka bi damutanensa a karkace,Waɗanda suke cewa, “Salama,”sa'ad da suke da abinci,Amma sukan kai yaƙin shahadaGa wanda bai ba su abin sawa a bakaba.
6 Saboda haka kome zai zama dareda duhu, ba wahayi ko duba.Rana za ta fāɗi a kan annabawa,Yini zai zama musu duhu baƙiƙirin.