3 Kuna cin naman mutanena, kunafeɗe fatar jikinsu,Kuna kakkarya ƙasusuwansu,Kuna yanyanka su gunduwagunduwa kamar naman da za a saa tukunya.”
4 Sa'an nan za su yi kuka ga Ubangiji,Amma Ubangiji ba zai amsa musuba.Zai ɓoye musu fuskarsa a wannanlokaci,Saboda mugayen ayyukansu.
5 Ga abin da Ubangiji ya ce a kanannabawan da suka bi damutanensa a karkace,Waɗanda suke cewa, “Salama,”sa'ad da suke da abinci,Amma sukan kai yaƙin shahadaGa wanda bai ba su abin sawa a bakaba.
6 Saboda haka kome zai zama dareda duhu, ba wahayi ko duba.Rana za ta fāɗi a kan annabawa,Yini zai zama musu duhu baƙiƙirin.
7 Masu gani za su sha kunya,Masu duba kuwa za su ruɗe,Dukansu za su rufe bakinsu,Gama ba amsa daga wurin Allah.
8 Amma ni ina cike da iko,Da Ruhun Ubangiji,Da shari'a da ƙarfin hali,Don in sanar wa Yakubu da laifinsa,Isra'ila kuma da zunubinsa.
9 Ku ji wannan, ya ku shugabanninjama'ar Yakubu,Da ku sarakunan mutanen Isra'ila,Ku da kuke ƙyamar shari'ar gaskiya,Kuna karkatar da dukan gaskiya.