1 “Ku ji abin da ni Ubangijinake cewa,Tashi ku gabatar da ƙararku agaban duwatsu,Ku bar tuddai su ji muryarku.
2 “Ku duwatsu da madawwaman tussanduniya,Ku ji tuhumar da Ubangiji yake yimuku.Gama Ubangiji, yana da maganagāba da mutanensa,Zai tuhumi Isra'ila.
3 “Ya ku jama'ata, me na yi muku?Wace irin fitina nake yi muku?Ku amsa mini!
4 Gama na fito da ku daga ƙasarMasar,Na fanshe ku daga gidan bauta.Na aika muku da Musa, da Haruna,da Maryamu.
5 Ya ku jama'ata, ku tunaDa abin da Balak, Sarkin Mowab, yaƙulla,Da yadda Bal'amu ɗan Beyor yaamsa masa,Da abin da ya faru daga Shittim, harzuwa Gilgal,Don ku san ayyukan adalci naUbangiji.”
6 Da me zan zo gaban Ubangiji,In sunkuyar da kaina a gaban Allahna Sama?Ko in zo gabansa da maraƙi banaɗaya domin yin hadaya taƙonawa?