1 Tawa ta ƙare, gama na zamakamar lokacin da aka gamatattara amfanin gona,Kamar lokacin da aka gama kalar'ya'yan inabi,Ba nonon inabi da za a tsinka, a ci,Ba kuma 'ya'yan ɓaure da sukaharba wanda raina yake so.
2 Mutanen kirki sun ƙare a duniya,Ba nagarta a cikin mutane.Dukansu suna kwanto don su zub dajini.Kowa yana farautar ɗan'uwansa datarko.
3 Sun himmantu su aikata abin da yakemugu da hannuwansu.Sarki da alƙali suna nema a ba suhanci,Babban mutum kuma yana faɗar sonzuciyarsa,Da haka sukan karkatar da zance.
4 Mutumin kirkinsu kamar ƙaya yake,Mai gaskiyarsu kuwa kamar shingenƙaya yake.Ranar da kuka sa mai tsaro,A ran nan za a aukar muku dahukunci.Yanzu ruɗewarku ta zo,
5 Kada ka dogara ga maƙwabcinka,Kada kuma ka amince da abokinka.Ka kuma kame bakinka dagamatarkaWadda take kwance tare da kai.