23 Sarki ya yi wa shugabannin mawaƙa umarni da ƙarfi a kan abin da za su yi kowace rana.
24 Fetahiya ɗan Meshezabel, daga zuriyar Zera na kabilar Yahuza, shi ne wakilin sarki a kan dukan abin da ya shafi jama'a.
25 Game da ƙauyuka da gonakinsu kuma, waɗansu mutanen Yahuza suka zauna a Kiriyat-arba, da Dibon da ƙauyukanta, da Yekabzeyel da ƙauyukanta,
26 da a biranen Yeshuwa, da Molada, da Bet-felet,
27 da Hazar-shuwal, da Biyer-sheba da ƙauyukanta,
28 da Ziklag, da Mekona da ƙauyukanta,
29 da En-rimmon, da Zora, da Yarmut,