1 Firistoci da Lawiyawa da suka komo tare da Zarubabel ɗan Sheyaltiyel, da Yeshuwa, su neSeraiya, da Irmiya, da Ezra,
2-7 Amariya, da Malluki, da Hattush,Shekaniya, da Rehum, da Meremot,Iddo, da Ginneton, da Abaija,Miyamin, da Mawadiya, da Bilga,Shemaiya, da Yoyarib, da Yedaiya,Sallai, da Amok, da Halkiya, da Yedaiya.Waɗannan su ne shugabannin firistoci da 'yan'uwansu a zamanin Yeshuwa.
8-9 Lawiyawa su ne,Yeshuwa, da Binnuyi, da Kadmiyel,Sherebiya, da Yahuza, da Mattaniya wanda yake lura da waƙoƙin godiya, da shi da 'yan'uwansa.Bukbukiya da Unno, 'yan'uwansu, suka tsaya daura da su a taron sujada.
10 Yeshuwa shi ne ya haifi Yoyakim, Yoyakim ya haifi Eliyashib, Eliyashib ya haifi Yoyada.
11 Yoyada ya haifi Jonatan, Jonatan ya haifi Yadduwa.