35 Sa'an nan waɗansu 'ya'yan firistoci, masu busar ƙaho, su ne Zakariya ɗan Jonatan, jīkan Shemaiya. Sauran kakanninsa su ne Mattaniya, da Mikaiya, da Zakkur, daga zuriyar Asaf.
36 Sauran 'yan'uwansa su ne Shemaiya, da Azarel, da Milalai, da Gilalai, da Ma'ai, da Netanel, da Yahuza, da Hanani. Suna da kayayyakin bushe-bushe da na kaɗekaɗe. Ezra magatakarda ne yake gabansu.
37 A Ƙofar Maɓuɓɓuga kuwa, sai suka yi gaba sosai wajen matakan birnin Dawuda, wajen hawan garu, daga bisa gidan Dawuda, zuwa Ƙofar Ruwa wajen gabas.
38 Ƙungiyar jama'a ta biyu ta masu yin waƙoƙin godiya, ta bi ta wajen hagu. Na bi su tare da rabin jama'a a kan garu, sama da Hasumiyar Tanderu zuwa garu mai fādi,
39 da Kuma sama da Ƙofar, Ifraimu da wajen Tsohuwar Ƙofar, da wajen Ƙofar Kifi, da Hasumiyar Hananel, da Hasumiyar Ɗari zuwa Ƙofar Tumaki, sai suka tsaya a Ƙofar Tsaro.
40 Haka fa ƙungiyoyi biyu ɗin nan masu raira waƙoƙin godiya suka tsaya a Haikalin Allah.Ni da rabin shugabanni muna tare da su.
41 Tare da firistoci kuma, wato su Eliyakim, da Ma'aseya, da Miniyamin, da Mikaiya, da Eliyehoyenai, da Zakariya, da Hananiya, suna busa ƙaho,