42 da kuma Ma'aseya, da Shemaiya, da Ele'azara, da Uzzi, da Yehohanan, da Malkiya, da Elam, da Ezer, suna raira waƙoƙi, Yezrahiya kuma shi ne shugabansu.
43 Jama'a suka miƙa hadayu da yawa a wannan rana, suka yi murna, gama Allah ya faranta musu zuciya ƙwarai. Mata da yara kuma suka yi murna. Aka ji muryar murnar mutanen Urushalima daga nesa.
44 A ran nan aka sa mutanen da za su lura da ɗakunan ajiya, da sadakoki, da nunan fari, da zaka. Su ne za su tara nunan fari daga gonakin da suke kusa da garuruwa, bisa ga yadda doka ta ce, saboda firistoci da Lawiyawa, gama mutanen Yahuza sun yi murna saboda hidimar da firistoci da Lawiyawa suka yi.
45 Sun yi wa Allahnsu sujada, sun yi hidimar tsarkakewa tare da mawaƙa da masu tsaron ƙofofi kamar yadda Dawuda da ɗansa Sulemanu suka umarta.
46 A dā a zamanin Dawuda da Asaf akwai shugaban mawaƙa, akwai kuma waƙoƙin yabo da na godiya ga Allah.
47 A zamanin Zarubabel da zamanin Nehemiya dukan jama'ar Isra'ila suka biya wa mawaƙa da masu tsaron ƙofofi bukatarsu ta kowace rana. Sun kuma ba Lawiyawa sadokoki, su Lawiyawa kuma suka ba zuriyar Haruna nasu rabo.