11 Malkiya ɗan Harim, da Hasshub ɗan Fahat-mowab suka gyara wani sashi da kuma Hasumiyar Tanderu.
12 Kusa da su kuma, sai Shallum ɗan Hallohesh mai mulkin rabin yankin Urushalima ya yi gyare-gyare tare da 'ya'yansa mata.
13 Hanun da mazaunan Zanowa suka gyara Ƙofar Kwari. Sun gina ta, suka sa ƙyamarenta, da sandunan ƙarfe na kulle ƙofofinta, da ƙyamarenta, suka gyara garun kamu dubu, har zuwa Ƙofar Juji.
14 Malkiya ɗan Rekab, mai mulkin yankin Bet-akkerem, ya gyara Ƙofar Juji. Ya gina ta, ya sa ƙyamarenta da sandunan ƙarfe na kulle ƙofofinta.
15 Sai Shallum ɗan Kolhoze, mai mulkin yankin Mizfa ya gyara Ƙofar Maɓuɓɓuga, ya gina ta, ya rufe ta, ya sa ƙyamarenta, da sandunan ƙarfe na kulle ƙofofinta. Ya kuma gina garun Tafkin Siluwam na gonar sarki, har zuwa matakan da suka gangaro daga Birnin Dawuda.
16 Bayansa kuma Nehemiya, ɗan Azbuk, mai mulkin yankin Bet-zur ya yi gyare-gyare, har zuwa wani wuri daura da kabarin Dawuda, har zuwa haƙaƙƙen tafki da gidan masu tsaro.
17 Waɗannan Lawiyawa sun yi gyare-gyare a ƙarƙashin shugabancin Rehum ɗan Bani.Kusa da su kuma, sai Hashabiya mai mulkin rabin yankin Kaila, ya yi gyare-gyare domin yankinsa.