4 Kusa da su kuma, sai Meremot ɗan Uriya, wato jīkan Hakkoz ya yi gyare-gyare.Kusa da shi kuma sai Meshullam ɗan Berikiya jikan Meshezabel ya yi gyare-gyare.Kusa da shi kuma sai Zadok ɗan Ba'ana ya yi gyare-gyare.
5 Kusa da Zadok kuwa mutanen Tekowa suka yi nasu gyare-gyare, amma manyansu ba su sa hannu ga aikin shugabanninsu ba.
6 Yoyada ɗan Faseya, da Meshullam ɗan Besodeya, suka gyara Tsohuwar Ƙofa, suka kafa katakanta, suka sa ƙyamarenta, da sandunan ƙarfe na kulle ƙofofinta.
7 Kusa da su kuma sai Melatiya Bagibeyone, da Yadon Bameronote, da mutanen Gibeyon, da na Mizfa waɗanda suke a ƙarƙashin mulkin Yammacin Kogin Yufiretis suka yi gyare-gyare.
8 Kusa da su kuma sai Uzziyel ɗan Harhaya, maƙerin zinariya, ya yi gyare-gyare.Kusa da Uzziyel kuma sai Hananiya, ɗaya daga cikin masu yin turare, ya yi gyare-gyare. Suka gyare Urushalima har zuwa Garu Mai Faɗi.
9 Kusa da su kuma sai Refaya ɗan Hur, mai mulkin rabin yankin Urushalima, ya yi gyare-gyare.
10 Kusa da Refaya kuma, sai Yedaiya ɗan Harumaf ya yi gyare-gyare daura da gidansa.Kusa da Yedaiya sai Hattush ɗan Hashabnaiya ya yi gyare-gyare.