7 Ga shi, ka sa annabawa su yi shelarka a Urushalima cewa, ‘Akwai sarki a Yahuza.’ To, za a faɗa wa sarki wannan magana, sai ka zo mu yi shawara tare a kan wannan al'amari.”
8 Sai na mayar masa da amsa cewa, “Faufau, ba a yi wani abu haka kamar yadda ka faɗa ba, kai ne ka ƙaga wannan a zuciyarka.”
9 Gama dukansu so suke su tsoratar da mu, suna cewa, “Za su daina aikin.” Amma na yi addu'a, na ce, “Ya Allah, ka ƙarfafa ni.”
10 Sa'ad da na ziyarci Shemaiya ɗan Delaiya, wato jikan wanda aka hana shi fita, sai ya ce mini, “Bari mu tafi cikin Haikalin Allah, mu rufe ƙofofin Haikalin, gama suna zuwa su kashe ka, za su iya zuwa a wani dare su kashe ka.”
11 Sai na ce, “Mutum kamata ne, zai gudu? Mutum irina zai shiga Haikali don ya tsere? To, ba zan tafi ba.”
12 Na gane Allah bai aike shi wurina ba. Ya yi mini wannan magana domin Tobiya da Sanballat sun haɗa baki da shi.
13 Gama da wannan nufi ne suka haɗa baki, don in ji tsoro, in yi yadda suke so, in yi zunubi, da haka za su ba ni mugun suna, su yi mini ba'a.