13 Ka kuma sauka a bisa Dutsen Sinai,Ka yi magana da jama'arka a can,Ka ba su ka'idodin da suka dace,Da dokoki, da kyakkyawar koyarwa.
14 Ka koya musu su kiyaye Asabar ɗinka tsattsarka,Ka kuma ba su dokokinka ta hannun Musa bawanka.
15 Ka ba su abinci daga sama sa'ad da suka ji yunwa,Ruwa kuma daga dutse sa'ad da suka ji ƙishi,Ka faɗa musu su shiga su mallaki ƙasar da ka yi alkawari za ka ba su.
16 Amma kakanninmu suka yi fāriya, suka taurare,Suka ƙi yin biyayya da umarnanka.
17 Suka ƙi yin biyayya,Suka manta da dukan abin da ka yi,Suka manta da al'ajaban da ka aikata.Cikin fāriyarsu suka zaɓi shugaba,Don su koma cikin bauta a Masar.Amma kai Allah ne mai gafartawa,Kai mai alheri ne, mai ƙauna,Jinƙanka da girma yake, ba ka yashe su ba.
18 Ko sa'ad da suka yi wa kansu ɗan marakin zubi,Suka ce shi ne allahn da ya fisshe su daga Masar,Ai, sun yi maka ɓatanci, ya Ubangiji.
19 Amma ba ka rabu da su a hamada ba,Saboda jinƙanka mai girma ne.Ba ka kuwa kawar da girgije da wuta ba,Waɗanda suke nuna musu hanya dare da rana.