16 Amma kakanninmu suka yi fāriya, suka taurare,Suka ƙi yin biyayya da umarnanka.
17 Suka ƙi yin biyayya,Suka manta da dukan abin da ka yi,Suka manta da al'ajaban da ka aikata.Cikin fāriyarsu suka zaɓi shugaba,Don su koma cikin bauta a Masar.Amma kai Allah ne mai gafartawa,Kai mai alheri ne, mai ƙauna,Jinƙanka da girma yake, ba ka yashe su ba.
18 Ko sa'ad da suka yi wa kansu ɗan marakin zubi,Suka ce shi ne allahn da ya fisshe su daga Masar,Ai, sun yi maka ɓatanci, ya Ubangiji.
19 Amma ba ka rabu da su a hamada ba,Saboda jinƙanka mai girma ne.Ba ka kuwa kawar da girgije da wuta ba,Waɗanda suke nuna musu hanya dare da rana.
20 Ta wurin alherinka ka faɗa musu abin da ya kamata su yi,Ka ciyar da su da manna, ka ba su ruwa su sha.
21 Ka taimake su a jeji shekara arba'in,Ka ba su dukan abin da suke bukata,Ƙafafunsu ba su kumbura su yi musu ciwo ba.
22 “Ka sa sun ci al'ummai da mulkoki da yaƙi,Ƙasashen da suke maƙwabtaka da tasu.Suka ci ƙasar Sihon, Sarkin Heshbon,Da ƙasar Bashan, inda Og yake sarki.