6 Sa'an nan suka yi wannan addu'a, suka ce,“Kai kaɗai ne Ubangiji, ya Ubangiji,Kai ne ka yi samaniya da taurari da sararin sama.Kai ne ka yi ƙasa, da teku, da kowane abu da yake cikinsu,Ka ba dukansu rai,Ikokin samaniya sun rusuna suna maka sujada.
7 Kai ne, ya Ubangiji Allah, ka zaɓi Abram,Ka fito da shi daga Ur ta Kaldiyawa,Ka sāke sunansa ya zama Ibrahim.
8 Ka iske shi amintacce a gare ka,Ka kuwa yi masa alkawari.Ka yi alkawari za ka ba shi ƙasar Kan'ana,Da ta Hittiyawa, da ta Amoriyawa, da ta Ferizziyawa,Da ta Yebusiyawa, da ta Girgashiyawa,Ta zama inda zuriyarsa za su zauna.Ka kuwa cika alkawarinka, gama kai mai aminci ne.
9 Ka ga wahalar kakanninmu a Masar,Ka ji kukansu a Bahar Maliya.
10 Ka kuma aikata alamu da al'ajabai a kan Fir'auna,Da fadawansa duka, da mutanen ƙasarsa,Gama ka san yadda suka yi wa jama'arka danniya.Ta haka ka yi wa kanka suna kamar yadda yake a yau.
11 Ka yi hanya ta cikin teku domin jama'arka,Ka sa su bi ta ciki a kan sandararriyar ƙasa.Ka sa waɗanda suke fafararsu suka hallaka cikin zurfin teku,Suka nutse kamar dutse.
12 Da rana ka bishe su da al'amudin girgije,Da dare ka bishe su da al'amudin wuta.