8 Ni Ubangiji na ce, “A ranar da zanhukunta Edom,Zan hallaka masu hikimarka,Zan shafe hikima daga dutsenIsuwa.
9 Jarumawanka za su firgita, yaTeman,Za a kashe kowane mutum dagadutsen Isuwa.
10 “Saboda kama-karyar da ka yi waYakubu ɗan'uwanka,Za a sa ka ka sha kunya,Za a hallaka ka har abada.
11 A ranan nan ka tsaya kawai,A ranar da abokan gāba suka fasaƙofofinsa.Suka kwashe dukiyarsa,Suka jefa kuri'a a kan Urushalima.Ka zama kamar ɗaya daga cikinsu.
12 Ba daidai ba ne ka yi murnaSaboda wahalar da ta samiɗan'uwanka.Ba daidai ba ne ka yi farin cikiSaboda halakar mutanen Yahuza.Ba daidai ba ne ka yi musu dariyaA ranar wahalarsu.
13 Ba daidai ba ne ka shiga ƙofarjama'ataA ranar da suke shan masifa.Ba daidai ba ne ka yi murnaA kan bala'in ɗan'uwanka.Ba daidai ba ne ka washe dukiyarsaA ranar masifarsa.
14 Ba daidai ba ne ka tsaya a mararraba,Don ka kashe waɗanda suke ƙoƙarintserewa.Ba daidai ba ne ka ba da waɗandasuka tsere a hannun maƙiyansuA ranar wahala.”