1 Ƙafafunki suna da kyau da takalmi,Ke mafificiyar budurwa!Tsarin cinyoyinki kamar aikin gwanin sassaƙa ne.
2 Cibinki kamar finjali ne, wanda bai taɓa rasa gaurayayyen ruwan inabi a ciki ba.Kwankwasonki kamar damin alkama ne a tsakiyar bi-rana.
3 Mamanki kamar bareyi biyu ne, wato tagwayen barewa ne.
4 Wuyanki kamar hasumiyar hauren giwa ne.Idonki kamar tafki ne cikin birnin Heshbon,Kusa da ƙofar Bat-rabbim.Hancinki kyakkyawa ne kamar hasumiyar Lebanon ta tsaron Dimashƙu.
5 Kin ɗaga kanki sama kamar Dutsen Karmel.Kitsattsen gashin kanki kamar shunayya mafi kyau ne,Yakan kama hankalin sarki.
6 Ke kyakkyawa ce ƙaunatacciyata,Kina sa ni jin daɗi a rai.