12 Ku shuka wa kanku adalci,Ku girbe albarkun ƙauna,Ku yi kautun saurukanku,Gama lokacin neman Ubangiji ya yi,Domin ya zo, ya koya muku adalci.
13 Kun shuka mugunta,Kun girbe rashin adalci,Kun ci amfanin ƙarya.“Da yake dogara ga hanyarku da ɗumbun sojojinku,
14 Domin haka hayaniyar yaƙi za ta tashi a tsakanin jama'arku.Dukan kagaranku za a hallaka su.Kamar yadda Shalmanesar ya hallaka Bet-arbel a ranar yaƙi.An fyaɗa uwaye da 'ya'yansu a ƙasa.
15 Haka za a yi muku, ya mutanen Betel, saboda yawan muguntarku.Da asuba za a datse Sarkin Isra'ila.”