1 “A lokacin da Isra'ila yake yaro, na ƙaunace shi,Daga cikin Masar na kirawo ɗana.
2 Yawan kiransu, yawan tayarwar da suke yi mini,Sai ƙara miƙa wa Ba'al sadaka suke yi,Suna ƙona turare ga gumaka.
3 Ko da yake ni ne na koya wa Ifraimu tafiya.Na ɗauke su a hannuna,Amma ba su sani ni ne na lura da su ba.
4 Na bishe su da linzamin alheri da ragamar ƙauna,Na zama musu kamar wanda yake ɗauke musu karkiya daga muƙamuƙansu.Na sunkuya, na ciyar da su.
5 “Ba su koma ƙasar Masar ba,Amma Assuriya za ta zama sarkinsuGama sun ƙi yarda su koma wurina.
6 Takobi zai ragargaje biranensu,Zai lalatar da sandunan ƙarafan ƙofofinsu,Zai cinye su domin muguwar shawararsu.
7 Mutanena sun himmantu su rabu da ni,Ko da yake an kira su ga Ubangiji,Ba wanda ya girmama shi.